AU Ta Cimma Matsaya Kan Tsaron Teku
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12508-au_ta_cimma_matsaya_kan_tsaron_teku
Shugabannin kasashe da gwamnatoci na kungiyar tarayyar Afrika (AU) sun cimma wani kundi kan tsaron teku da ci gaba a Afrika, a yayin wani zaman taro a birnin Lome na kasar Togo.
(last modified 2018-08-22T06:59:05+00:00 )
Oct 16, 2016 02:20 UTC
  • AU Ta Cimma Matsaya Kan Tsaron Teku

Shugabannin kasashe da gwamnatoci na kungiyar tarayyar Afrika (AU) sun cimma wani kundi kan tsaron teku da ci gaba a Afrika, a yayin wani zaman taro a birnin Lome na kasar Togo.

Makasudin wannan kundin doka, da shugabanni da gwamnatocin AU suka rattaba hannu kansa shi ne na yin rigakafi da murkushe manyan laifuffuka na cikin gida da na kasa da kasa musammun ma ta'addanci, fashin teku, fataucin miyagun kwayoyi, fataucin mutane, da kamun kifi ba bisa doka ba da sauransu.

A cewar wannan kundin, kowace kasar dake ciki ta dauki niyyar cigaba da kokarinta ta hanyar daukar matakan da suka dace domin samar da ayyukan yi, rage talauci, bada kwarin gwiwa wajen fadakar da jama'a kan batutuwan teku ta yadda za a kafa wani yanayin rayuwa da karfafa hadin kan jama'a ta hanyar aiwatar da wata siyasa mai kyau, da zummar warware matsalolin tattalin arziki da na jama'a.