An cimma matsayar farko a tattaunawar kasar Kwango
Jam'iyun siyasa da kungiyoyin fararen hula A kasar Demokaradiyar kwango sun cimma matsayar farko a tattaunawar da suke yi na fidda kasar daga rikicin siyasa
Kimanin Mahalarta tattaunar ta 'yan kasa 13 suka amince da wannan kudiri, kuma ana sa ran a ranar 18 ga wannan wata na Oktoba da muke ciki, kudirin zai samu amincewar dukkanin wakilan 'yan siyasa da kungiyoyin fararen hula. bisa wannan sabon kudiri, an bayyana cewa Shugaba Joseph kabila zai ci gaba da zama a kan karagar milki har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe a watan Avrilun shekarar 2018, sannan kuma bangare 'yan adawa za su riki mikaman Piraministan har zuwa wancan lokaci.
A nasa bangare Alexis Thambwe Mwamba Ministan Shara'a na kasar ya ce tattaunawar ta samu amincewar wani bangare na 'yan adawa. a baya dai an shirya cewa za a gudanar da zaben shugaban kasar ta Kwango a watan gobe, saidai Gwamnati ta dage zaben saboda matsalar rashin kudi kamar yadda ta bayyana, saidai bangaren 'yan adawa sun zarki Shugaba Joseph Kabila da yin haka domin dawwama a kan karagar milki.