Libya: Martanin Majalisar Dinkin Duniya Akan Harin Tripoli
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12544-libya_martanin_majalisar_dinkin_duniya_akan_harin_tripoli
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya A Kasar Libya Ya yi tir da Harin da aka kai wa cibiyoyin gwamnati a Tripoli
(last modified 2018-08-22T06:59:05+00:00 )
Oct 16, 2016 15:45 UTC
  • Libya: Martanin Majalisar Dinkin Duniya Akan Harin Tripoli

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya A Kasar Libya Ya yi tir da Harin da aka kai wa cibiyoyin gwamnati a Tripoli

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya A Kasar Libya Ya yi tir da harin da aka kai wa cibiyoyin gwamnati a Tripoli.

Tashar telbijin din al-hadath, ta ambato wakilin musamman na majalisar dinkin duniya a kasar Libya Martin Kobler yana yin tir da harin da aka kai wa wasu cibiyoyin gwmanatin hadin kan kasa a birnin Tripoli.

Kobler  ya kirayi dukkanin bangarorin al'ummar kasar da su kai zuciya nesa wajen haddasa rikici.

An kafa gwamnatin hadin kan kasar Libya ne daga gwamnatoci biyu da kasar ta  yi a baya a  biranen Tripoli da kuma tobroq.