Rikicin Kabilanci Ya Jikkata Mutane Da Dama A Kasar Sudan Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1261-rikicin_kabilanci_ya_jikkata_mutane_da_dama_a_kasar_sudan_ta_kudu
Wani sabon rikicin kabilanci da ya kunno kai a garin Pibor da ke jihar Jonglei a kasar Sudan ta Kudu ya jikkata mutane akalla 35 tare da hasarar dukiyoyi.
(last modified 2018-08-22T06:57:51+00:00 )
Feb 25, 2016 08:57 UTC
  • Rikicin Kabilanci Ya Jikkata Mutane Da Dama A Kasar Sudan Ta Kudu

Wani sabon rikicin kabilanci da ya kunno kai a garin Pibor da ke jihar Jonglei a kasar Sudan ta Kudu ya jikkata mutane akalla 35 tare da hasarar dukiyoyi.

Kungiyar Likitoci ta Dokters Without Borders ta sanar da cewa: Rikicin kabilancin ya fara ne tun daga ranar Talata har zuwa jiya Laraba a garin Pibor da ke jihar Jonglei na kasar Sudan ta Kudu, inda ya janyo jikkatan mutane akalla 35 tare da tilastawa wasu fiye da 1000 tserewa da muhallinsu zuwa sansanin 'yan gudun hijira da ke karkashin kulawar Malajisar Dinkin Duniya.

Har ila yau Kungiyar Litocin ta Doctors Without Borders ta tabbatar da kona gidaje masu yawa a garin na Pibor tare da kokawa kan karacin magunguna a kasar ta Sudan ta Kudu.