RDC : 'Yan Adawa Sunyi Watsi Da Yarjejeniyar Siyasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12628-rdc_'yan_adawa_sunyi_watsi_da_yarjejeniyar_siyasa
Jam'iyyar adawa mai tarihi a jamhuriya demukuradiyyar Congo tayi wasti da yarjejeniyar da kawancen jam'iyyu masu mulki suka cimma da wasu sirarun jam'iyyun adawa wacce ta tanadi dage zaben shugaban kasar har zuwa watan Afrilu na shekara 2018.
(last modified 2018-08-22T06:59:06+00:00 )
Oct 18, 2016 13:12 UTC
  • RDC : 'Yan Adawa Sunyi Watsi Da Yarjejeniyar Siyasa

Jam'iyyar adawa mai tarihi a jamhuriya demukuradiyyar Congo tayi wasti da yarjejeniyar da kawancen jam'iyyu masu mulki suka cimma da wasu sirarun jam'iyyun adawa wacce ta tanadi dage zaben shugaban kasar har zuwa watan Afrilu na shekara 2018.

Jagoran jam'iiyar ta UDPS, Etienne Tshisekedi ya yi fatali da wannan yarjejeniya wace zata baiwa shugaban kasar mai barin gado Joseph Kabila damar ci gaba da kasancewa kan madafun iko duk da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya haramta masa da hakan kasancewar wa'addin mulkinsa na kawo karshe ne a ranar 20 ga watan Desamba mai zuwa.

Dama kafin hakan kawancen 'yan adawan da jam'iyyar ta UDPS ke jagoranta ya ki amunce shiga tattaunawar kasa da ka fara a ranar 1 ga watan Satumba daya gabata a Kinshasa babban birnin kasar da nufin samun mafita kan rikicin siyasa kasar domin gudanar da zabubuka cikin lumana.

Yarjejeniyar da aka cimma a jiya Litinin tare da wakilai daga bangarori daban daban ta tanadi baiwa shugaba J. Kabila damar da ci gaba da mulkin kasar har zuwa bayan karshen wa'addin mulkinsa da kuma shirya zaben shugaban kasa da aka dage har zuwa watan Afrilu na shekara ta 2018. 

Idan ana tune a ranakun 19 zuwa 20 ga watan Satumba daya gabata kimanin mutane 50 ne suka rasa rayukansu a rikicin daya barke tsakanin jami'an tsaro da masu kin jinin tazarcen shugaba Joseph kabila.