Mayakan Boko Haram sun kaiwa Sojojin Najeriya Hari a Jihar Borno
An yi musayar wuta tsakanin mayakan kungiyar boko haram da Sojojin Najeriya a jihar Borno dake shiyar arewa maso gabashin kasar
A wata sanarwa da kakakinta Rundunar Sojin Kasa ta Najieriya Kanar Sani Kukasheka Usman ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a yammacin jiya Talata inda mayakan na boko haram suka kai hari a garin Gashiga na jhar Borno mai iyaka da jumhoriyar Nijar.
Sanarwar ta kuma ce sojoji 13 ne suka jikkata a harin, sannan kuma wasu suka bata, saidai kakakin bai bayyana adadin Sojojin da suka bace ba, sannan kuma ya ce tuni aka baza sojoji domin gano wadanda suka bacen.
Wannan sanarwar na zuwa ne bayan da kungiyar Boko Haram din da ke da alaka da kungiyar IS ta sanar da cewa ta kashe sojojin Najeriya 20, bayan jikkata wasu da dama na daban a yayin hari da suka kai wa sojojin hadin gwiwa na Najeriya da Nijer a garin na Gashiga,a nasa bangare Kanar Sani Kukasheka Usman ya yi watsi da wannan rahoto.
Tun daga shekarar 2009 ne ,Najeriya ta fara fuskantar hare-haren ta'addancin Boko haram a shiyar arewa maso gabashin Najeriya, inda sanu a hankali rikicin ya watsu zuwa kasashen dake makobtaka da ita, daga farkon shekarar 2015 din da ta gabata, Sojojin Kasashen Chadi, kamaru da Najeriya suka fara aiki tare na kawar da kungiyar boko haram din kafin daga bisani a kafa rundunar hadin gwiwa wacce ta hada kasashen Najeriya, Nijer, Kamaru, Chadi da Benin domin kawar da wannan kungiyar ta ta'addanci.