Ashabab ta sake kai wani hari a Somaliya
Kungiyar Ashabab ta kai hai wani mumunan hari a kusa da birnin Magadushu fadar milkin kasar Somaliya
Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa ya habata cewa harin da kungiyar Ashabab ta kai garin Afgoye mai nisan kilomita 30 daga arewa maso gabashin birnin Magadushu ya yi sanadiyar mutuwar akalla fararen hula 10 da kuma jami'an 'yan sanda 4,kungiyar ta kai harin ne da nufin tarwatsa wani wurin bincike na 'yan sanda,inda suka kutsa da wata mota makare da bama-bamai cikin ofishin 'yan sandar kafin daga bisani a yi dauki ba daki tsakanin jami'an tsaron kasar da mayakan Ashabab din.
Wani Jami'in 'yan sanda ya sanar da cewa bayan da dakarun wanzar da zaman Lafiya na kungiyar Afirka da ake kira Amisson suka kawo dauki mayakan Kungiyar Ashabab din mai alaka kut da kut da kungiyar Alka'ida sun fice daga cikin garin.
A nasa bangare Kakakin kungiyar ta al shabaab Sheikh Abdi asis Abu Musab ya tabbatar da kai wannan hari sannan kuma ya ce yanzu haka suna rike da yankuna masu yawa a kasar ta Somaliya.