Habasha: Ci gaba da yin Zanga-zangar Kin Jinin Gwamanti
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12658-habasha_ci_gaba_da_yin_zanga_zangar_kin_jinin_gwamanti
Ana ci gaba da yin zanga-zanga A Habasha
(last modified 2018-08-22T06:59:06+00:00 )
Oct 19, 2016 08:45 UTC
  • Habasha: Ci gaba da yin Zanga-zangar Kin Jinin Gwamanti

Ana ci gaba da yin zanga-zanga A Habasha

Ana ci gaba da yin Zanga-zangar kin jinin gwamnati a kasar Habasha.

A yau laraba an yi zanga-zanga mai tsanani a yankin Oromo, sai dai gwamnatin kasar ta  yi kira da a kawo karshenta.

Wasu rahotanni daga kasar sun ce jami'an tsaro sun kame wasu masu zanga-zanga da dama.

Ma'aikatar tsaron kasar ta Habasha ta ce, tana sa ido da bin diddigin hanyoyin sadarwar da masu zanga-zangar su ke amfani da ita.

Al'ummar Oromo dai suna yin Zanga-zanga ne domin nuna kin amincewarsu da abinda su ka kira rashin samar da daidaito ta fuskar tattalin arziki da raba mukamai a tsakanin 'yan kasa.

Mutane 55 ne aka kashe a zanga-zangar da aka yi a baya.