Kungiyar Ecowas Tana Murna Da Samun Nasarar Tattaunawar Kasar Guine Bissau.
Kasar Guinea Konakry Ta Shiga Tsakanin Rikicin Siyasar Guinea Bissau
Kungiyar tattalin arziki ta kasashen yammacin Afirka, "Ecowas" ta bayyana gamsuwarta akan nasarar da aka samu ta bude tattaunawar bangarorin siyasar kasar Guinea Bissau.
A makon da ya shude ne dai bangarorin siyasar kasar ta Guinea Bissau da su ka hada da gwamnati da 'yan hamayya sun yi taro domin warware sabanin da ke tsakaninsu.
Shugaban kasa Guinea Konakry Alpha Konde ne ya zama mai shiga tsakanin, yan hamayyar kasar Guinea Bissau, da kuma shugaban kasa, Mario Wava.
Kungiyar ta Ecowas ta aike da sakon taya murna ga shugabannin kasashen Guinea Bissau da kuma Guinea Konakry akan tattaunawar.
Shekara daya kenan dai da harkokin tattalin arzikin kasar ta Guinea Bissau su ka tsaya cak, dambaruwar siyasar kasar.