Yunkurin juyin milkin da bai ci nasara ba a kasar Burkina Faso
Gwamnatin Burkina Faso ta sanar da wani yunkurin kifar da Gwamnati daga bangare tsofin jami'an fadar shugaban kasar
A wata sanarwa da ya fitar a wannan Juma'a, Ministan cikin gidan kasar Burkina Faso Simon Campore ya ce wani gungu mai manbobi 30 ya yi yunkurin fitar da Sojojin dake tsare a gidan yari kan lafin yunkurin juyin milkin da bai ci nasara ba a shekarar 2015 din da ta gabata, sannan kuma su kai hari kan fadar shugaban kasar.
An bayyana cewa wannan gungu na mutane 30 tsofin Jami'an tsaron fadar shugaban kasa ne na Gwamnatin shugaba Blaise Canpore da ta gabata.
Bayan sama da shekaru 27 a kan karagar milki Blaise Campore Tsohon Shugaban kasar ta Burkina Faso ya fuskanci zanga-zanga daga Al'ummar kasar lamarin da ya sanya Sojoji suka yi masa juyin milki a shekarar 2014, kuma a halin da ake ciki yana gudun hijra a kasar Iviry Coast.