Shugaba Jacob Zuma Na Afirka Ta Kudu Ya Isa Burundi
Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta kudu ya isa kasar Burundi a wannan Alhamis, inda zai jagoranci wata babbar tawagar kungiyar tarraya Afirka a wunkurin ganin an farfado da tattaunawa tsakanin gwamnatin da 'yan adawa na Burundi.
Ko baya ga Mr Zuma, akwai shugabanin kasahen Afirka da suka hada da na Mauritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz, da Macky Sall na Senegal, da na kasar Gabon Ali Bongo Ondimba da kuma firaministan kasar Habasha Haile Mariam Dessalegn duk dai a yunkurin shawo kan rikicin siyasa da yaki -ci -yaki cincewa a kasar ta Burundi.
Wannan dai na daga cikin matakin da aka dauka a taro baya-bayan nan na kungiyar (AU) domin samun mafita a rikicin kasar ta Burundi.
Ko a ranar Litinin din nan data gabata, idan ana tune babban sakatare na MDD Ban-ki-monn ya gana da shugaban kasar ta Burindi Pierre Nkurunziza wanda ya masa alkawarin farfado da wata sabuwar tattaunawar ta neman kawo karshen rikici a wannan kasa.