Najeriya : An Tsawaita Shirin Yaki Da Masu Fashin Jiragen Ruwa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12760-najeriya_an_tsawaita_shirin_yaki_da_masu_fashin_jiragen_ruwa
 Gwamnatin Najeriya ta sanar da kara wa'adin watanni 3 na farautar bata gari dake fashin manyan jiragen ruwa a tekunan kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:07+00:00 )
Oct 22, 2016 02:46 UTC
  • Najeriya : An Tsawaita Shirin Yaki Da Masu Fashin Jiragen Ruwa

 Gwamnatin Najeriya ta sanar da kara wa'adin watanni 3 na farautar bata gari dake fashin manyan jiragen ruwa a tekunan kasar.

Babban hafsan sojojin ruwan kasar ne Ibok-Ete Ibas, ya tabbatar da hakan a garin Onne na jihar Rivers dake kudancin kasar, inda ya kara da cewa, sojojin ruwan kasar sun taka rawa wajen dakile hare haren da tsageru ke kaddamarwa kan manyan jiragen ruwa a tekunan kasar.

Mista Ibas ya ce tura jiragen ruwan yaki masu yawa da gwamnati ta yi zuwa yankin, ya taimaka sosai wajen samun wannan nasara.

A cewarsa, dakarun sojin ruwan kasar na ci gaba da sintiri domin dakile aniyar ba ta garin dake fashin jiragen ruwa a tekunan kasar, musamman a yankin da ake jigilar danyen man kasar.

hakan dai a cewar Mista Ibas zai taimakawa manyan jiragen ruwan 'yan kasuwa damar gudanar da zirga zirgarsu ba tare da fuskantar wata matsala ba, da kuma kare arzikin mai da iskar gas na kasar domin inganta samar da kudaden shiga.