Najeriya : Bom Ya Kashe 'Yan Sanda Hudu A Yola
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1279-najeriya_bom_ya_kashe_'yan_sanda_hudu_a_yola
Rahotanni daga Najeriya na cewa 'yan sanda hudu ne suka rasa rayukan su, sakamakon fashewar wani bom a hedkwatar 'yan sanda na birnin Yola dake arewa maso gabashin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:57:52+00:00 )
Feb 25, 2016 13:55 UTC
  • Najeriya : Bom Ya Kashe 'Yan Sanda Hudu A Yola

Rahotanni daga Najeriya na cewa 'yan sanda hudu ne suka rasa rayukan su, sakamakon fashewar wani bom a hedkwatar 'yan sanda na birnin Yola dake arewa maso gabashin kasar.

ko baya ga wadanda suka rasa rayukan sun akwai wasu akalla shida da suka jikkata kamar yadda jagoran kungiyar agajin gaggawa ta NEMA a yankin Mal. Sa'ad Bello ya shaidawa kanfanin dilancin labaren faransa na AFP .

Kakakin ma'aikatar 'yan sanda Adamawa Othman Abubakar ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa bom din ya tashi ne bisa kuskure a cikin wani wajen aje makaman yaki a wani sashe na jami'an kula tono ababe masu tarwatsewa.

kasalika a cewar jami'in sun saba kama ire-iren wadanan ababen masu fashewa kuma ayi bincike kan su kafin a adana su, saidai wannan daya shafe ba'a yi nasara lalata shi ba yadda ya kamata kafin a aje shi, yakan kuma yasa ya tarwatse bisa hadari.

jami'in ya kuma kara da cewa tashin bom din baya da wata nasaba da harin Boko haram.