Mayakan Kungiyar Al-Shabab Sun Mamaye Wani Garin Mai Muhimmanci A Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12832-mayakan_kungiyar_al_shabab_sun_mamaye_wani_garin_mai_muhimmanci_a_somaliya
Mayakan kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab na kasar Somaliya sun mamaye wani gari mai muhimmanci bayan janyewar sojojin kasar Habasha daga garin.
(last modified 2018-08-22T06:59:07+00:00 )
Oct 23, 2016 11:56 UTC
  • Mayakan Kungiyar Al-Shabab Sun Mamaye Wani Garin Mai Muhimmanci A Somaliya

Mayakan kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab na kasar Somaliya sun mamaye wani gari mai muhimmanci bayan janyewar sojojin kasar Habasha daga garin.

Majiyar tsaron Somaliya a ta bakin Muhammad Nur Adan daya daga cikin jami'an tsaron kasar a garin Beledweyne ta sanar da cewa: Mayakan kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab sun mamaye garin Halgan da ke tsakiyar kasar bayan janyewar sojojin kasar Habasha daga garin.

Garin Halgan shi ne gari na uku da sojojin Habasha suka fice daga ciki a kasar Somaliya a karkashin shirin gwamnatin Habasha na janye sojojinta daga Somaliya bayan kammala wa'adin aikinsu na wanzar da zaman lafiya a kasar karkashin jagorancin dakarun kungiyar tarayyar Afrika na "AMISON".

A kasa da mako guda sojojin Habasha sun janye daga garuruwan Moqokori da El-Ali gami da garin na Halgan. Kasar Habasha dai tana da sojoji 4,400 da suke taimakawa sojojin gwamnatin Somaliya a fagen yaki da mayakan kungiyar Al-Shabab a kasar.