An Samu Gawar Wani Jami'in Diflomasiyyar Saudiyya A Morocco
Oct 23, 2016 15:57 UTC
Kafofin yada labaran kasar Morocco sun bayar da rahoton samun gawar wani jami'in diflomasiyyar Saudiyya a cikin wani gida a garin Barshid da ke arewa maso yammacin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Fars ya bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron kasar ta Morocco sun samu rahoto daga jama'a bayan da aka kwashe kimanin kwanaki hudu ana jin wari daga wani gida a wata unguwar masu hannu da shuni a garin na Barshid, inda aka samu jami'in na diflomasiyyar Saudiyya.
Jami'in tsaron kasar Morocco sun ba a san dalilin mutuwar mutumin ba, amma dai an shiga gudanar da bincike kan lamarin, domin gano hakikanin abin da ya faru.
Tags