Burkina Faso : An Zargi Mutanen Compaore Da Kokarin Yin Juyin Mulki
(last modified Mon, 24 Oct 2016 17:21:26 GMT )
Oct 24, 2016 17:21 UTC
  • Burkina Faso : An Zargi Mutanen Compaore Da Kokarin Yin Juyin Mulki

Jam'iyya mai mulki a Burkina faso ta zargi mutanen tsohon shugaban kasar Blaise Compaore da yunkurin yin juyin mukin wa shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore.

A ranar Juma'a data gabata ce gwamnatin Burkina faso ta sanar da murkushe wani yunkurin juyin mulki a farkon wannan wata.

Jam'iyyar MPP mai mulki a kasar dai ta zargi tsohuwar rundinar tsaron fadar shugaban da shirya juyin mulkin t ahanyar farmawa barikin sojin kasar inda ake tsare da wadanda ake zargi da shirya wacen juyin mulkin.

Jam'iyyar ta kara da cewa ko bayyanar da hambararen shugaban kasar Blaise Compaore ya yi a gidajen talabijin a baya bayan nan akwai wata manufa a ciki.

ko baya ga hakan a acewarsa akwai wasu sojojin tsofuwar  rundinar ta RSP da suka shigo kasar daga ketare dauka kayan aiki da kuma makuden kudade wanda yake nuna karara sun samu ganawa da jagoran nasu dake gudun hijira a waje.