Kulla Yarjeniyoyi 20 A Tsakanin Kasashen Tanzania Da Moroko.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12961-kulla_yarjeniyoyi_20_a_tsakanin_kasashen_tanzania_da_moroko.
Ziyarar Sarkin Moroko A Tanzania
(last modified 2018-08-22T06:59:08+00:00 )
Oct 26, 2016 02:54 UTC
  • Kulla Yarjeniyoyi 20 A Tsakanin Kasashen Tanzania Da Moroko.

Ziyarar Sarkin Moroko A Tanzania

Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato cewa; Sarkin Moroko Muhammad Sadisu, da shugaban kasar Tanzania John Pombe Magufuli,  sun rattana hannu akan yarjeniyoyi 20 a jiya talata a birnin  Darussalam.

Yarjeniyoyin dai sun shafi hanyoyin  bunkasa alaka da kuma zuba hannun jari a cikin kasuwannin kasashen biyu. Haka nan kuma yawon bude ido da noma da ma'adanai da kasuwanci da alakar bankunan da kiwon lafiya. Sai kuma jiragen kasa.

Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magufuli, ya bayyana yarjejeniyar da cewa; Wani sabon ginshiki ne na alakar kasashe a nahiyar Afirka.

Bugu da kari, ya kuma bayyana ziyarar ta sarkin Moroko a kasarsa da cewa; masomin bude sabon shafi ne a alakar kasashen biyu.

Sarkin Morokon dai yana ziyarar ne a kasashen Rwanda da Tanzania da kuma Habasha.