Harin Ta'addanci A Somaliya Ya ci Rayuka Da Dama A Somaliya.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i12967-harin_ta'addanci_a_somaliya_ya_ci_rayuka_da_dama_a_somaliya.
al-Shaban Sun Kai Hari a Sansanin Rundunar Tarayyar Afirka
(last modified 2018-08-22T11:29:08+00:00 )
Oct 26, 2016 06:27 UTC
  • Harin Ta'addanci A Somaliya Ya ci Rayuka Da Dama A Somaliya.

al-Shaban Sun Kai Hari a Sansanin Rundunar Tarayyar Afirka

Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua ya amabto kakakin rundunar tabbtar da zaman lafiya ta Afirka da ke kasar Somaliya Joe Kibet, yana cewa; A jiya talata kungiyar al-shabab ta kai wa wani sansaninsu hari da ke harin Beledweyne a arewa da birnin Magadishu.

Kibet ya ci gaba da cewa; Sojojinsu biyu da kuma farar hula guda ne su ka rasa rayukansu, yayin da su kuma su ke kashe maharan da su ka kai 10.

Kibet ya ce; Maharan na al-shabab sun bude wuta da bindigogi akan sansanin, kafin daga baya wani ya tarwatsa mota mai makare da bama-bamai.

al-Shabab ta dauki alhakin kai harin, sannan ta sanar da cewa ta kashe sojojin kasar Djibouti 17.

Tuni dai shugaban kasar ta Somaliya Hassan Sheikh Muhammad ta yi tir da harin na al-shabab.

Da akwai sojojin kasashen Afirka da su ka kai 22,000 da su ke fada da al-shabab a cikin Somaliya.