Za'a Sake Dawo Da Kujerar Priminister A Kasar Sudan
Wata majiyar gwamnatin kasar Sudan ta bayyana cewa shugaban kasar Umar Hassan Al-Bashir ya bukaci a dawo da kujerar Priminister a tsarin siyasar kasar
Majiyar muryar Jumhuriyar musulunci ta Iran daga birnin Khartun ta nakalto wani babban Jami'in gwamnatin Sudan yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa shugaban yana bukatar a dawo da wannan kujerar nan da watannin biyu masu zawa. Bayan juyin mulkin da shugaba Albashir ya jagoranta a shekara ta 1989 ne ya shafe kujerar Priminister a tsarin siyasar kasar, inda kafin haka Sadik Almahdi ne Priministan kasar ta Sudan a lokacinda ya yi wa gwamnatinsu juyin mulki.
Gwamnatin shugaba Albashir dai ta fara wani shiri na sasantawa da jam'iyyun yan adawa da kuma kungiyoyin yan tawaye a kasar daga cikin watan Octoban shekara ta 2015 har zuwa watan Octoba da muke ciki. Mafi yawan jam'iyyun adawar kasar dai sun haramta sasantawan sun kuma yi watsi da shirin gaba daya.
Sannan tun shekara ta 2009 ne kotun kasa da kasa ta ICC ta bada sammashin kama shugaba Albashir kan laifuffukan yaki a yankin darfur don haka ne yake kokarin dinke baraka a cikin gida don bashi damar ci gaba da shugabancin kasar wanda kuma zai ci gaba da zama kariya a gareshi daga fadawa hannun kotun.