Yan Adawar Mauritaniya Sun Bukaci Bude Zaman Tattaunawa Da Gwamnatin Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13006-yan_adawar_mauritaniya_sun_bukaci_bude_zaman_tattaunawa_da_gwamnatin_kasar
Wasu daga cikin jam'iyyun adawar Mauritaniya sun bukaci bude wani sabon fagen tattaunawa tsakaninsu da gwamnatin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:08+00:00 )
Oct 27, 2016 07:03 UTC
  • Yan Adawar Mauritaniya Sun Bukaci Bude Zaman Tattaunawa Da Gwamnatin Kasar

Wasu daga cikin jam'iyyun adawar Mauritaniya sun bukaci bude wani sabon fagen tattaunawa tsakaninsu da gwamnatin kasar.

A daidai lokacin da jam'iyyun adawa a Mauritaniya suke neman sake bude zaman tattaunawa da bangaren gwamnatin kasar kan matsalolin da suke ci gaba da addabar kasar, a gefe guda kuma jam'iyya mai mulki a Mauritaniya tana ci gaba da jaddada bukatar gudanar da zaben jin ra'ayin jama'ar kasar ne kan neman gudanar da gyarar fuska wa kundin tsarin mulkin kasar ta Mauritaniya.

Gwamnatin Mauritaniya karkashin jagorancin shugaba Muhammad Wuld Abdul-Aziz dai tana bukatar ganin an soke Majalisar Dattijan kasar daga cikin kundin mulkin Mauritaniya tare da maye gurbinsa da Majalisun gundumomi, don haka take bukatar samun goyon bayan manyan jam'iyyun adawa domin cimma burinta.