Dokar ta bace a arewa maso gabashin kasar Kenya.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13015-dokar_ta_bace_a_arewa_maso_gabashin_kasar_kenya.
Gwamnatin kasar Kenya ta sanya dokar hana shigi da fici na tsahon kwanaki 60 a garin Mandera dake arewa maso gabashin kasar
(last modified 2018-08-22T06:59:08+00:00 )
Oct 27, 2016 14:35 UTC
  • Dokar ta bace a arewa maso gabashin kasar Kenya.

Gwamnatin kasar Kenya ta sanya dokar hana shigi da fici na tsahon kwanaki 60 a garin Mandera dake arewa maso gabashin kasar

A wata sanarwa da ya fitar a wannan Alkhamis Ministan cikin gidan Kenya Mista Joseph Ole NKaissery ya ce cikin makuni uku da suka gabata garin na Mandera ya fuskanci hare-haren ta'addanci daga kungiyar Ashabab ta kasar Somaliya, domin haka ya zamanto wajibi Gwamnati ta dauki matakin kare Al'ummar yanki, saboda da haka ne Gwamnatin ta ga ya dace ta dauki wannan mataki domin baiwa Jami'an tsaro damar gudanar da aiyukan su kamar yadda ya kamata kuma wannan doka ta hana shigi da fici za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 27 ga watan Decemba.

A ranar talatar da ta gabata mayakan Ashabab sun kai wani mumunan hari cikin wata Otel dake cikin garin na Mandera, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 12, kuma wannan shi ne hari na biyu da mayakan Ashabab din suka cikin wannan gari kasa da makunni uku.

Sanarwa ta ce cikin Makun farko dokar ta shafi dukkanin kauyuka da kuma yankunan da suka kewaye garin a tsahon kilomita 20 da kuma kauyukan dake isa zuwa iyakar kasar da Somaliya.

A bangare guda Jami'an dake tsaron Ofishin Jakadancin Amurka dake birnin Nairobi fadar milkin kasar Kenya sun bindige wani Matasi har lahila, hakan kuwa na zuwa ne bayan da matashin ya yanki wani Mutum a gaban Ofishin.