Kenya : An Kafa Dokar Hana Fita A Mandera
Gwamnatin Kenya ta kafa dokar hana fita ta wattani biyu a yankin Mandera dake arewa maso gabashin kasar inda aka fuskanci hare-haren tsagerun Al'shabab a ranar Talata data gabata.
Dokar data fara aiki a jiya Alhamis ta tanadi hana fitar dare daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe daga ranar ta 27 ga watan Oktoba zuwa 27 ga watan Disamba shekara nan.
A ranar Talata data gabata ce wani harin bam da kungiyar Al'shabab ta dauki alhakin kaiwa yayi sanadiin mutuwar 12 a wani karamin Otel an Mandera, lamarin daya tilastawa gwamnan yankin Ali Roba kira ga mahukuntan kasar dasu karfafa matakan tsaro saboda abunda ke faruwa a yankin.
Yau kusan watanni uku kenan da yankin arewa maso gabashin Kenya ke fuskantar hare-hare da ake dangatawa dana kungiyar Al'shabab, inda ko a ranar 6 ga watan nan na Oktoba wani dan bindiga ya kashe muta shida a wani gini da ma'aikatan gine gine keda zama.
Tun dai bayan da ta shiga yaki da kungiyar Al'shabab ta Somaliya a shekara 2011, kasar Kenya ke fuskantar hare-hare martani daga Al'shabab, mafi muni a cikinsu sun hada da wanda kungiyar ta kai a cibiyar kasuwancin nan ta Westgate dake Nairobi da kuma na jami'ar Garissa dake gabashin kasar.