An sako daruruwan yara daga hanun jami'an tsaron Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13075-an_sako_daruruwan_yara_daga_hanun_jami'an_tsaron_najeriya
Daraktan Asusun yara na MDD UNICEF dake kula da yammaci gami da tsakiyar Afirka ya sanar da sakin daruruwan yara daga hanun jami'an tsaron Najeriya.
(last modified 2018-08-22T06:59:09+00:00 )
Oct 29, 2016 02:18 UTC
  • An sako daruruwan yara daga hanun jami'an tsaron Najeriya

Daraktan Asusun yara na MDD UNICEF dake kula da yammaci gami da tsakiyar Afirka ya sanar da sakin daruruwan yara daga hanun jami'an tsaron Najeriya.

Kafar watsa labaran Jaridar Le Figaro ta kasar Faransa ta nakalto Manuel Fontaine babban Daraktan Asusun yara na MDD UNICEF dake kula da yammaci gami da tsakiyar Afirka na cewa a wannan Juma'a an sako wasu yara 876 daga hannun jami'an tsaro , a birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya, a sakamakon wata tattaunawa da suka yi da su.

Jami'in asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce, ana tsare ne da yaran a barikin soji, bisa zarginsu da alaka da kungiyar Boko Haram, a baya dai yaran na zama ne a wasu yankuna da ke karkashin ikon kungiyar boko haram.

Mista Fontaine ya ce Dakarun tsaron Najeriya na ci gaba da kama kananen yara a yankunan da suka kasance kalkashin mamayar kungiyar boko haram a baya, lamarin da ya fuskancin nuna adawa daga kungiyoyin kare hakin bil-adama.

Sojojin Najeiryan ba su yi bayyani ba dangane da wannan lamari, saidai magabatan kasar sun bayyana cewa a kwai bukatar yin tambayoyi ga matasan domin gano mayakan boko haram daga cikin su.