Yan Adawa A Mauritaniya Sun Bukaci Shugaban Kasar Da Ya Yi Murabus
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1309-yan_adawa_a_mauritaniya_sun_bukaci_shugaban_kasar_da_ya_yi_murabus
Shugaban jam'iyyar adawa ta the Rally of Democratic Forces (RFD) a kasar Mauritaniya ya bukaci shugaban kasar da yayi murabus daga kan mukaminsa.
(last modified 2018-08-22T06:57:52+00:00 )
Feb 26, 2016 05:51 UTC
  • Yan Adawa A Mauritaniya Sun Bukaci Shugaban Kasar Da Ya Yi Murabus

Shugaban jam'iyyar adawa ta the Rally of Democratic Forces (RFD) a kasar Mauritaniya ya bukaci shugaban kasar da yayi murabus daga kan mukaminsa.

A taron gangamin da shugaban jam'iyyar adawa ta "RFD" a Mauritaniya Ahmed Wuld Daddah ya gudanar a birnin Nouakchott fadar mulkin kasar ya gabatar da kira ga shugaban kasar Mohammad Wuld Abdul-Aziz kan ya hanzarta yin murabus daga kan mukaminsa saboda al'ummar Mauritaniya sun kosa da irin bakar siyasar gwamnatinsa kuma ba zasu ci gaba da juriya fiye da haka ba.

Ahmed Wuld Daddah ya kara da cewa: Samun canjin gwamnati a Mauritaniya ya karato domin al'umma ba zasu ci gaba da juriya fiye da irin mummunan halin da suke ciki ba a halin yanzu.