Shugaban Kasar Kenya Ya Kai Ziyarar Aiki A Sudan Kan Koton ICC
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13123-shugaban_kasar_kenya_ya_kai_ziyarar_aiki_a_sudan_kan_koton_icc
Karamin ministan harkokin wajen kasar Sudan ya bayyana cewa ziyarar da shugaban kasar Kenya ya kai birnin Kharthum yana da muhimmanci matuka.
(last modified 2018-08-22T06:59:09+00:00 )
Oct 30, 2016 03:44 UTC
  • Shugaban Kasar Kenya Ya Kai Ziyarar Aiki A Sudan Kan Koton ICC

Karamin ministan harkokin wajen kasar Sudan ya bayyana cewa ziyarar da shugaban kasar Kenya ya kai birnin Kharthum yana da muhimmanci matuka.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya nakalto Kamal Isamail yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyata ya gana da shugaba Umar Hassan Al-bashir kan batun yiyuwan ficewar kasar Sudan daga kotun kasa da kasa ta ICC kwatakwata.

Ziyarar Uhuru Kenyata zuwa Sudan ta zo ne bayan mako guda da kiran da gwamnatin Sudan tayi wa  dukkan kasashen Africa na su fice daga kotun ta kasa da kasa.

A ranar 21-Octoban shekarar da muke ciki ne Sudan ta jingine aiki tare da kotun ta ICC  bayan da kasar Africa ta kudu ta katse huldarta da ita. Bayan haka ne kasashen Burundi da kuma Gambia suka bi sahu suka bayyana ficewarsu daga kotun.

Tun lokacin da aka kafa kutun ta kasa da kasa dai ta hukunta mutane daga kasashen duniya goma, amma tara daga cikinsu daga nahiyar Africa ne, da wannan dalilin ne shuwagabannin Africa suke sukan wannan kotun kan nuna ware a cikin aikinta.