Shugaban Kasar Burkina Faso Ya Kira Kan Daura Damarar Yaki Da Ta'addanci
(last modified Sun, 30 Oct 2016 10:29:40 GMT )
Oct 30, 2016 10:29 UTC
  • Shugaban Kasar Burkina Faso Ya Kira Kan Daura Damarar Yaki Da Ta'addanci

Shugaban kasar Burkina Faso ya yi kira ga al'ummar kasarsa kan daura damarar yaki da duk wani aikin ta'addanci a duk fadin kasar.

A jawabinsa da ya gabatar ga al'ummar Burkina Faso a sakon murnar cikan shekaru biyu da kawo karshen mulkin kama karya ta shugaba Blaise Compore ta hanyar gidan talabijin din kasar a jiya Asabar; Shugaba Roch Marc Christian Kabore ya yi kira ga al'ummar Burkina Faso kan bude fagen yaki da duk wani aikin ta'addanci a duk fadin kasar; yana mai fayyace cewa; Magoya bayan tsohon shugaban kasar suna aiwatar da nau'o'in ayyukan ta'addanci a fagen siyasa da zamantakewan al'umma, don haka babu amana tsakanin al'ummar Burkina Faso da 'yan ta'adda.

Har ila yau Shugaban kasar ta Burkina Faso ya yi furuci da cewa: Manufar 'yan ta'addan siyasar kasar ita ce kunna wutar rikici da tashe-tashen hankula da kokarin yin kafar ungulu ga tafiyar tsarin dimokaradiyya a kasar.