Ivory Coast : 'Yan Adawa Na Zargin Magudi A Zaben Raba Gardama
A kasar Ivory Coast, a yayin da al'ummar kasar ke bayyana ra’ayin su a zaben raba gardama dangane da batun yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, 'yan adawa tuni suka fara zargin yunkurin tafka magudi a zaben na yau Lahadi.
Shugaban kasar Alassane Ouattara ne ya shigar da wannan bukata domin kawo gyarawa kundin tsarin mulkin kasar, batun da 'yan adawa suka jima suna korafi akai da cewa ya sabawa tsarin demukuradiyya a kasar.
Duk da hakan dai 'yan adawa sun yi kira zuwa ga magoya bayan su na gani sun kada kuri’ar kin amincewa da haka.
Rahotanni daga kasar sun nuna cewa an samu 'yan matsaloli daga nan zuwa cen a runfunan zabe inda wasu gungun matasa suka tada yamutsi a wasu runfunan zabe tare da yin awan gaba da akwatinan zabe, duk da cewa dai gwamnatin kasar ta ce an shawo kan wadanan matsalolin.
Kafin hakan dai gwamnatin kasar ta dau kwararen matakan tsaro domin gujewa duk wani tashin hankali da zai iya faruwa musamen a wasu mayan biranen kasar da suka hada da Abidjan,Bouake,Yamoussokro.