Shugaban Kenya Ya Jadadda Bukatar Bunkasa Kasashen Yankin Gabashin Afrika
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13177-shugaban_kenya_ya_jadadda_bukatar_bunkasa_kasashen_yankin_gabashin_afrika
Shugaban kasar Kenya ya jaddada bukatar bunkasa harkar tattalin arziki da na siyasa a tsakanin kasashen yankin gabashin Afrika.
(last modified 2018-08-22T06:59:10+00:00 )
Oct 31, 2016 07:35 UTC
  • Shugaban Kenya Ya Jadadda Bukatar Bunkasa Kasashen Yankin Gabashin Afrika

Shugaban kasar Kenya ya jaddada bukatar bunkasa harkar tattalin arziki da na siyasa a tsakanin kasashen yankin gabashin Afrika.

A ziyarar aikin da ya kai kasar Sudan; Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya jaddada wajabcin karfafa matakan siyasa da na tattalin arziki tsakanin kasarsa da Sudan; Yana mai fayyace cewa siyasar harkokin wajen kasar Kenya ta ginu ce a kan kokarin bunkasa alaka a dukkanin bangarori tsakaninta da sauran kasashen yankin gabashin Afrika.

Uhuru Kenyatta ya kai ziyarar aiki na kwanaki biyu zuwa Sudan ne sakamakon gayyata na musamman da ya samu daga shugaban kasar Umar Hasan Albashir a kokarin da kasashen biyu ke yi na bunkasa alaka a tsakaninsu.