Za a kawo karshen rikicin siyasa a kasar Ethiopia
Ministan tsaron kasar Habasha ya tabbatar da cewa za a kawo karshen rikicin siyasa cikin gaggawa a kasar
Kafar watsa labaran Afirka News ta nakalto Mr Siraj Fegessa Ministan tsaron kasar Habasha na cewa wajibi ne dukkanin kungiyoyin siyasa su kawo karshen zanga-zangar da suke yi a kasar kadda su yi amfani da siyasa wajen kawo tashin hankali da rashin tsaro a kasar.
Ministan ya ce ya zuwa yanzu an sako kimanin Mutane dubu biyu da aka kama a rikicin baya bayan nan bayan da Gwamnati ta yi musu afuwa, zanga-zanga a kasar Habashan na kara munana ne tun bayan da Gwamnati ta haramta duk wata zanga-zanga da kuma taruwar Al'umma a fadin kasar baki daya.
Rahoton ya ce mafi yawan Mutanan da aka kama a yankin Aroumuya na garin Sabata ne. zanga-zangar kin jinin gwamnati na kara karuwa a yankin ne saboda sabanin siyasa da kuma na kabilanci dake akwai a yankin.