Shugaba Buhari ya gana da shugabannin Niger Delta
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin yankin Niger Delta, da nufin kawo karshen hare-haren masu tada kayar baya kan bututan mai a yankin.
A yayinda yake ganawa da shugabannin kungiyar al'ummomin yankin Niger Delta , Shugaba Buhari ya fito karara ya shaida masu cewa ba yadda za'a cimma biyan bukatunsu idan kasar na fama da rashin zaman lafiya.
Shugaba Buhari ya bayyana wa shugabannin cewa barnar da ake yi a yankinsu ta isa. A matsayinsu na shugabanni dole su tashi su magance tashin hankali da ake fama da shi a yankin, kada su dinga cewa duk wata matsala daga Abuja ake haddasata. sannan kuma yace su je su ga abun da zasu iya yi a kai. idan kuma suka gaza babu yadda za'a ga martabarsu a matsayinsu na shugabanni.
Shugaba Buhari ya kara da cewa tilas ne sai akwai zaman lafiya da kwanciyar hankalin sannan za'a samu wadata da masu saka jari su shigo kasar. amma matukar ana tada zaune tsaye babu wata gwamnati da zata iya gamsar da masu saka jari su shigo kasar
A nasu bangare, Shugabanin Niger-Daltan sun gabatar da na su bukatun,inda suka bukaci a dinga sasu a harkokin man fetur, ana damawa dasu. A basu damar hakan man fetur ko kuma a baiwa gwamnatocin jihohinsu damar hakowar. Sun kuma kira a sake duba yadda ake rabon arzikin kasa musamman kudaden da kasar ke samu daga man fetur domin suma suna bukatar su ci moriyar abun da Allah ya azurta kasar su da shi