Zanga-zangar Nuna Adawa Da Cin Hanci Da Rashawa A Kasar Kenya
Nov 03, 2016 14:27 UTC
Daruruwan Mutane Sun yi Zanga-zanga a kasar Kenya
Masu Zanga-zangar a birnin Nairobi suna nuna yin tir da yaduwar cin hanci da rashawa da aka bankado a ma'aikatar lafiya.
Kamfanin dillancin labarun Reuters, ya nakalto cewa; Daruruwan masu zanga-zangar suna nuna fushinsu ne akan rahoton da aka fitar dangane da zargin sama da fadi da kudaden da aka yi wa ma'aikatar lafiya ta kasar.
Jami'an tsaron kasar sun tarwatsa masu zanga-zangar ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye.
Tuni dai ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta karyata tuhumar da kafafen watsa labarun kasar su ka yi mata na sama da fadi da kudade.
Tags