Cimma Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Yankin Galkayo Na Kasar Somaliya
Shugaban kasar Somaliya da wakilin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar sun bayyana jin dadinsu kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a yankin Galkayo tsakanin al'ummun lardunan Galmudug da na Puntland.
Shugaban kasar Somaliya Hasan Sheikh Mahmud da wakilin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Michael Keating sun bayyana jin dadinsu kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a tsakanin al'ummun lardunan Galmudug da na Puntland kan sabani dangane da mallakar yankin Galkayo.
Shugaban kasar Somaliya Hasan Sheikh Mahmud ya jaddada yin kira ga mahukuntan lardunan na Galmudug da na Puntland da su mutunta yarjejeniyar da suka cimma na kawo karshen tashe-tashen hankula a tsakaninsu. Kamar yadda a nashi bangaren wakilin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Somaliya Michael Keating ya jaddada yin kira ga al'ummun lardunan biyu kan kawo karshen duk wani nau'in rikici a tsakaninsu.
Tun bayan bullar rikici tsakanin al'ummun lardunan Galmudug da na Puntland kan mallakar yankin Galkayo an samu hasarar rayuka tare da tilastawa mutane kimanin 50,000 barin muhallinsu.