Al'Shabab Babbar Barazana Ce Ga Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13435-al'shabab_babbar_barazana_ce_ga_somaliya
MDD ta fitar da wani rahoto wanda a cikinsa ta bayyana cewa kungiyar Al'shabbab na ci gaba da kasancewa babbar barazana ga kasar Somaliya, cin hanci da kuma rashin kwarewar sajojin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:11+00:00 )
Nov 05, 2016 14:42 UTC
  •  Al'Shabab Babbar Barazana Ce Ga Somaliya

MDD ta fitar da wani rahoto wanda a cikinsa ta bayyana cewa kungiyar Al'shabbab na ci gaba da kasancewa babbar barazana ga kasar Somaliya, cin hanci da kuma rashin kwarewar sajojin kasar.

A cikin rahoton data fitar Jiya Juma'a MDD ta ce har yanzu Al'shabab nada karfin shirya kai hare hare yankin.

haka zalika a cikin rahoton, kwararu na MDD sun kalubalanci yadda matsalar cin hanci ke kara kamari a wannan kasa, koda yake MDD ta yaba da ci gaban da aka samu ta wajen hana fitar da gwal daga kasar wanda ke zamen wata hanya ta samun kudi na kungiyar ta Al'shabab.

Rahoto ya kuma kalubalanci yadda har yanzu aka kasa samun ingantacen tsaro a kasar ta Somaliya, duba da yadda kungiyar keda karfin kai hare hare har kan dakarun wanzar da zamen lafiya na AMINSOM, koda yake rahoton ya ce kungiyar ta rage karfi wajen kai hare hare a yankin.

Kungiyar Al'shab dai ta jima tana aikata ayukan ta'addi a gabshin Afrika inda so tarin yawa takan kai hare haren ta kan dakarun AMISOM da kuma cikin kasar Kenya.