Taron Ministocin Noma na kasashen Larabawa da Afirka a kasar Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13465-taron_ministocin_noma_na_kasashen_larabawa_da_afirka_a_kasar_sudan
An fara gudanar da Taron Ministocin Noma na kasashen Larabawa da Afirka a kasar Sudan
(last modified 2018-08-22T06:59:11+00:00 )
Nov 06, 2016 07:41 UTC
  • Taron Ministocin Noma na kasashen Larabawa da Afirka a kasar Sudan

An fara gudanar da Taron Ministocin Noma na kasashen Larabawa da Afirka a kasar Sudan

Tashar Telbijin din Almanar ta kasar Labanon ta habarta cewa sama da wakilan kasashe Larabawa da na Afirka 65 ne ke halartar taron hadin gwiwa na Ma'aikatun Noma da nufin duba hanyoyin da ya kamata su bi na bunkasa aiyuka Noma a kasashen su zuwa 2030.

Wannan dai, shi ne karo na uku da kasashen ke yi da nufin tabbatar da amincin abinci gami da bunkasa harakokin Noma a kasashen su, baya ga hakan taron zai tabo batun kasuwanci da kuma sanya hanun jari  kan abinda ya shafi Noma a tsakanin kasashen.

Mahalta  taron sun ce za su tattauna kan batun sanya hanun jari a kasashen Afirka kan harakokin Noma daga bangaren kasashen Larabawa musaman ma kasashen da kasar su ke da kyau a aiyukan Noma to amma batun samun tabbaci a wannan bangare na da muhimancin gaske.

A nata bangare, Kungiyar Taryyar Afirka ta sanar da cewa dukkanin manbobin kungiyar a shirye suke wajen zartar da wannan shiri.