'Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-Zangar Jin Jinin Shugaban Guinea Bissau
(last modified Sun, 06 Nov 2016 17:36:36 GMT )
Nov 06, 2016 17:36 UTC
  • 'Yan Sanda Sun  Tarwatsa Masu Zanga-Zangar Jin Jinin Shugaban Guinea Bissau

'Yan sanda a kasar Guinea Bissau sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar kin jinin shugaban kasar da kuma kiran da a sake gudanar da zabe a daidai lokacin da kasashen yankin suke ta kokari wajen ganin an kawo karshen rikicin da ya kunno kai a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya  bayyana cewar masu zanga-zangar wadanda wasunsu suke dauke da kwalayen da suke kiran shugaban kasar Jose Mario Vaz da ya  sauka daga karagar mulki, sun nufin fadar shugaban kasar ne da ke garin Bissau, babban birnin kasar kamar yadda kuma suke kiran da a rusa  majalisar kasar da sake gudanar da zabe, inda 'yan sanda dauke da kayan fada suka tarwatsa su.

Wannan rikici dai ya biyo bayan da shugaba Jose Mario Vaz ya kori firayi ministan kasar  Domingos Simoes Pereira daga karagar mulki a wani abu da ake ganinsa a matsayin rikicin tabbatar da iko da ke gunada a cikin jam'iyyar PAIGC mai mulki.

A jiya dai shugabar kasar Liberiya uwargida Ellen Johnson Sirleaf ta tafi kasar Guinea Bissau a madadin kungiyar ECOWAS da nufin shiga tsakani da nufin kawo karshen rikicin da ya kunno kai,. Bayan tattaunawar dai kungiyar ECOWAS din ta bukaci da a cimma yarjejeniya ciki kuwa har da sake nada firayi ministan da zai sake kafa wata gwamnati.