An kai hari kan wasan kallon kafa a Sudan ta kudu
Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan yan wasan kollon kafa a kasar Sudan ta kudu.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto kakakin 'yan sanda na kasar Sudan ta kudu a yau Litinin ya sanar da mutuwar mutane 9 yayin harin da wasu 'yan bindiga suka kai kan masu kalon wasan kwalon kafa a daren Assabar din da ta gabata yayin da suka fito daga wani gida da ake nuna wasan kwalon kafa na kasashen turai ta hanyar telbiji dake gefen kudu masu yammacin Juba babban birnin kasar.
Kakakin 'yan sandar ya ce mutane 6 sun rasu ne a gidan kalon wasan , su kuma ukun sun rasu ne yayin da ake kokarin kaisu asibiti.
Har ila yau kakakin ya kara da cewa har yanzu sun kasa gano dalilin da ya sanya 'yan bindigar suka kai wannan hari ga ma'abota kalon wasan kwalon kafar.
Tun a karshen shekarar 2013 ne kasar Sudan ta kudun ta fada cikin rikici bayan da shugaba Salva keir ya kori mataimakinsa na farko Riek Machar.