Kungiyar Tarayyar Afirka ta dauki kudirin kawo karshen kungiyar Ashabab a Somaliya
Ofishin Dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka (Amison) dake kasar Somaliya ya tabbatar da cewa za ta karya lagon kungiyar Ashabab a kasar baki daya.
Ofishin ya ce Dakarun su dake jibke a yankuna daban daban na cikin kasar a shirye suke su karya lago da kuma tunkarar duk wata barazana na kungiyar Ashabab din kuma hakan ma ya zamanto wajibi domin tabbatar da tsaro a kasar.
Wannan sanarwa na zuwa ne yayin da aka nada Nuru Usman Suba garke a matsayin sabon Kwamandan kungiyar wanzar da zaman lafiya na tarayar Afirka a kasar Somaliyan da ake kira da Amisson.
Duk da cewa Kungiyar Amison din ta samu nasara da dama wajen tabbatar da tsaro a kasar Somaliyan, to amma har har yanzu kungiyar ta Ashabab na ci gaba da kai hare haren ta'addanci a kasar .