Ci gaba da zanga-zangar kin jinin Gwamnatin a Kasar Demokaradiyar Kwango
Zanga-zangar kin jinin Gwamnati ta yi tsanani a kasar Demokaradiyar kwango.
Rahotanni dake fitowa daga birnin Kinshasha na kasar Kwango na nuni da cewa zanga-zangar da ake ci gada da gudanarwa a wannan litinin ta rikide zuwa ga tashin hankali tsakanin jami'an 'yan sanda da magoya bayan 'yan adawa.
Kafin wannan zanga-zangar, jami'an 'yan sanda da ciboyoyin tsaron kasar sun bukaci dukkanin kungiyoyin siyasa na bangare adawa da magoya bayan su da su ku ji duk wani taro ko zanga-zanga a fadin kasar gaba daya.kafin hakan dai Gwamnati ta sanar da haarmta duk wata zanga-zanga da kuma taron Siyasa a fadin kasar.
Duk da irin jami'an 'yan sandar da aka jibke a lunui da sako na manyan buranan kasar bai hanawa 'yan adawar fitowa ba, lamarin da ya sa ake ci gaba da dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan 'yan adawar.