Bukatar Shawo Kan Matsalolin Tashe-Tashen Hankula A Kasar DR Congo
Wata cibiyar kare hakkin bil-Adama da habaka tsarin dimokaradiyya a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta bukaci daukan kwararan matakan ganin an shawo kan matsalolin tashe-tashen hankula a lardin Kivu ta Arewa da ke gabashin kasar.
Cibiyar kare hakkin bil-Adama da habaka tsarin dimokaradiyya ta "CEPADHO" a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta bayyana tsananin damuwarta kan yadda tashe-tashen hankula sukeci gaba da addabar garin Beni da ke lardin Kivu ta Arewa, don haka ta yi kira ga rundunar sojin kasar da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya kan hanzarta kai dauki garin da nufin dawo da doka da oda.
Cibiyar ta "CEPADHO" ta fayyace cewa: Lardin Kivu ta Arewa da ke gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ya zame tamkar cibiyar tashe-tashenhankula a kasar, inda ake kai hare-haren wuce gona da iri kan jami'an tsaro da aiwatar da kisan gilla kan fararen hula.