An sako Mutane da dama da aka kama kan zarkin boko haram
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13564-an_sako_mutane_da_dama_da_aka_kama_kan_zarkin_boko_haram
Wani babban jami'in Soja a Najeriya ya sanar da sakin sama da Mutane dubu guda da aka kama kan zarkin su a alaka da kungiyar Boko haram
(last modified 2018-08-22T06:59:12+00:00 )
Nov 08, 2016 07:29 UTC
  • An sako Mutane da dama da aka kama  kan zarkin boko haram

Wani babban jami'in Soja a Najeriya ya sanar da sakin sama da Mutane dubu guda da aka kama kan zarkin su a alaka da kungiyar Boko haram

Kamfanin dillancin labaran Xin huwa na kasar China ya nakalto Victor Ezugwu babban komandan Rundunar soja ta 7 a Najeriya  a wannan Litinin na cewa bayan gudanar da bincike Sojoji sun saki Mutane Dubu daya da 271 da ake tsare da su kan zarkin su nada alaka da Kungiyar boko haram a Jihar Borno dake shiyar arewa maso gabashin kasar.

Mista Victor Ezugwu ya kara da cewa mafi yawan mutanan da aka tsare tsakanin watan favrayu da watan Oktoba na wannan shekara ta 2016 da muke cikin an sake su, daga cikin su kuma a kwai Mata da kananen Yara.

Har ila yau komandan ya ce a yayin da suke tsare da mutanan sun kula da lafiyar su kuma suna basu abinci so uku a ko wata rana.