Saliyo Ta Yi Bikin Murnar Cika Shekara Guda Ba Ebola
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13591-saliyo_ta_yi_bikin_murnar_cika_shekara_guda_ba_ebola
A Jiya Litinin al'ummar kasar Saliyo sun yi bikin murnar ban kwana da cutar Ebola, tun bayan da hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana kasar a matsayin wacce ta yi nasarar kawar da cutar daga kasar shekara guda.
(last modified 2018-08-22T06:59:12+00:00 )
Nov 09, 2016 02:19 UTC
  • Saliyo Ta Yi Bikin Murnar Cika Shekara Guda Ba Ebola

A Jiya Litinin al'ummar kasar Saliyo sun yi bikin murnar ban kwana da cutar Ebola, tun bayan da hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana kasar a matsayin wacce ta yi nasarar kawar da cutar daga kasar shekara guda.

Domin munar wannan rana, jama'ar kasar ta Saliyo sun yi shigar kaya mai launin ruwan dorawa domin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a sanadiyyar cutar Ebola.

A jawabin da ya gabatar ga al'ummar kasar shugaba Ernest Bai Koroma, ya ce, al'ummar kasar sun fara aiki babu kakkautawa domin farfadowa daga ibtila'in da kasar ta fuskanta tun bayan bullar cutar ta Ebola mai saurin hallaka jama'a.

A hannu daya kuma shugaban ya yi tsokaci game da irin ta'annati da cutar ta yi ga rayuwar jama'a, da koma bayan tattalin arziki da kasar ta fuskanta.

Ya kara da cewa, mutane dubu 8 ne suka kamu da cutar a fadin kasar, kuma daga cikinsu mutane 3,589 sun rasa rayukansu, ciki har da ma'aikatan lafiya 221.