Ivory Coast : Yajin Aikin Ma'aikata Ya Samu karbuwa A Bangaren Ilimi
A kasar Ivory Coast yau kwana na biyu kenan da ma'aikatan gwamnati suka tsunduma cikin wani yajin aiki na kwanaki uku domin nuna fishinsu akan wani kuduri da ya shafi ma'aikatan da suka yi ritaya.
kudirin wanda aka amunce da shi tun a cikin shekara 2012 ya tanadi rage kudin fensho da kashi 30 zuwa 50 %, yayin da kuma shekarun zuwa ritaya suka karu daga 55 har zuwa 65 a babban mataki.
Rahotanni daga kasar sun nuna cewa yajin aikin ya fi samun karbuwa sosai a bangaren ilimi musamen a makarantun jami'o'i, kamar yadda wani jami'i a cikin wadanda suka shirya gwagwarmayar, Mista Théodore Zadi, ya shaidawa kanfanin dillancin labaren faransa na AFP.
Saidai a cewarsa yajin aikin bai samu karbuwa ba sosai a wasu bangarori, kamar a bangaren ma'aikatar kudi, aman duk da haka zasu ci gaba da gwagwarmaya.
Ma'aikatan dai sun ce wannan yajin aiki na gargadi ne don haka suna fatan gwamnatin kasar zata sauraresu.