An yanke hukunci dauri ga wasu Manoma a kasar Marokko
Bayan arangama tsakanin Manoma da 'yan sanda a kasar Marokko, kotu ta yanke hukunci dauri a gidan kaso ga wasu Manoma 18
Tashar Telbijin din Rusiya Alyaum ta nakalto Umar Arrabib wani jami'i a kungiyar kare hakin bil-adama ta kasar Marokko na cewa kotun yankin Satat dake tsakiyar kasar ta yanke hukuncin daurin shekaru 4 a gidan yari ga wasu manoma 7 yayin da ta yanke daurin shekaru uku ga wasu Manoman guda 11 kan zarkin su da taho mu gama tsakanin su da 'yan sandar kasar.
Arbib ya ce rikici tsakanin Manoma da 'yan sandar ya faru ne a ranar 26 ga watan Oktoban da ya gabata, kuma a yayin wannan rikici wasu mazauna kauyen sun jikkata yayin da aka cabke wasu da dama na daban.
Mazauna kauyen dai sun nuna adawarsu kan kwace musu filayen su na Noma da Gwamnatin kasar ta yi domin haka jami'in na kungiyar kare hakin bil-adama ya ce wannan hukunci da aka yankewa manoman ba abinda za su amince da shi ba ne, saboda laifin da suka aikata bai kai a yanke musu wannan hukunci ba.