An kame 'yan adawa a kasar Sudan
A yayin Zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin farashin Man fetir, jami'an 'yan sanda sun kame 'yan adawa 21 a kasar Sudan
A yayin zanga-zangar da manyan Jam'iyun adawa suka kira a kasar Sudan na nuna adawa da karin farashin Man fetir wanda ya janyo hauhawar kayan masarufi, jami'an 'yan sanda sun kame wasu jiga-jigan 'yan adawa kimanin 21 a birnin Khartum.
Babbar jam'iyar Adawa ta kasar watau Sudan Congress ta tabbatar da wannan labari, sannan kuma ta ce ci gaba da neman rikici daga jami'an tsaron kasar shi zai karar ruwa rikicin siyasar kasar,har ila yau Jam'iyar ta ce mafi yawa daga cikin mutanan da aka kame shugabanin Jam'iyar ne.
Bayan yin alawadai da wannan kamu, wasu daga cikin Jam'iyun adawa sun kira 'yan kasar da su shiga yajin aiki domin tilastawa Gwamnati ta sake tunani kan kudirin da ta dauka na kara kudaden Man fetir, da kuma wutar Lantarki a kasar.