Kame Masu Zanga-zanga A Kasar Murtaniya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13633-kame_masu_zanga_zanga_a_kasar_murtaniya
An Kame 'yan Masu Zanga-zanga a kasar Murtaniya
(last modified 2018-08-22T06:59:13+00:00 )
Nov 09, 2016 15:54 UTC
  • Kame  Masu Zanga-zanga A Kasar Murtaniya

An Kame 'yan Masu Zanga-zanga a kasar Murtaniya

Jami'an tsaron kasar Murtaniya sun kame  masu zanga-zanga fiye da 20.

Cibiyar watsa labaru ta Africa Time; ta nakalto cewa; a jiya talata ne jamian tsaron kasar su ka yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kulake domin tarwatsa masu zanga-zangar da su ke nuna kin amincewarsu da sauye-sauyen da aka yi a tashar jiragen ruwa.

Sauyin ya kunshi sauke manyan kontena-kontena a cikin birnin Nowakshort maimakon a bakin gabar ruwa.

Jami'an tsaron sun tarwatsa masu zanga-zangar tare da kame wasu daga cikinsu.