Kungiyar Amnesty Ta Bukaci Gwamnatin Lagos Ta Dakatar Da Rushe Rushe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13741-kungiyar_amnesty_ta_bukaci_gwamnatin_lagos_ta_dakatar_da_rushe_rushe
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnisty International a birnin Lagos ta Nigeria ta yi kira ga gwamnatin jihar Lagos ta dakatar da rusa gine gine a wasu yankuna na bakin ruwa a birnin, wanda ya zuwa yanzu mutane dubu 30 sun rasa matsuguni.
(last modified 2018-08-22T06:59:13+00:00 )
Nov 12, 2016 04:11 UTC
  • Kungiyar Amnesty Ta Bukaci Gwamnatin Lagos Ta Dakatar Da Rushe Rushe

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnisty International a birnin Lagos ta Nigeria ta yi kira ga gwamnatin jihar Lagos ta dakatar da rusa gine gine a wasu yankuna na bakin ruwa a birnin, wanda ya zuwa yanzu mutane dubu 30 sun rasa matsuguni.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa dubban mutane ne suka rasa matsugunansu dake bakin ruwa a birnin Lagos kuma idan har gwamnatin jihar tashi gaba da rushe rushe to kuwa fiye da mutane dubu 300 ne zasu rash wurin kwana.

Don haka kungiyar Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin jihar ta dakatar da wannan shiri na rusa gidajen matane sai bayan da kotu ta bayyana ra'ayinta a kai ko kuma ta samarwa mutanen wadan nan yankunan wasu wurare.

Gwamnatin jihar dai tace ta kudurin anniyar rusa dukkanin gine gine wadanda basa bisa ka'ida don maida birnin kamar yadda ka'idojin kasa da kasa suna tanada.

Hukumomin gwamnatiun jihar wadanda suke gudanar da aikin rushe rushen sun bayyana cewa zasu ci gaba da ayyukansu kamar yadda aka umrcesu, kuma sun musanta labarin da ke cewa sun yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu a lokacinda suke gudanar da wannan aikin. 

Birnin Lagos a Nigeria dai shi ne babbar cibiyar kasuwanci a kasar kuma tana da mazauna kimani miliyon 20.