Tashe Tashen Hankula Suna Kara Yawa A Kasar Sudan Ta Kudu
Majiyar labarai daga kasar sudan ta kudu sun bayyana cewa tashe tashen hankula suna kara yawaita a yankin kudu maso gabacin sudan ta kudu.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya nakalto kamfanin yada labarai na skynes yana bayyana haka a jiya jumma'a ya kuma kara da cewa, mayakan yan tawaye a garin Koyo wanda yake kan iyaka da kasar Uganda sun kara da sojojin gwamnatin a cikin yan kwanakin da suka gabata kuma mutane 20 suka rasa rayukansu a yayinsa wasu 20 kuma suka ji rauni.
Wani babban jami'an tsaro a yankin wanda bai son a bayyana sunansa ya ce yaki tsakanin bangarorin biyu a wannan yankin ya tilastawa mutane da dama barin gidajensu da kuma samun mafaka a wasu garuruwan kan iyaka na kasar da kasar Uganda.
A makonnon da suka gabata ne shugaban yan tawayen kasar sudan ta kudu Reik Marcher ya shaidawa wasu kafafayen yada labarai a birnin Khartun na kasar Sudan kan cewa zai fuskanci sojojin gwamnatin kasarsa da karfi har zuwa lokacinda za'a sami sauyin da ya dace.