Ministan Harkokin Wajen Kasar Italiya Ya Kai Ziyarar Aiki Jamhuriyar Nijar.
Nov 12, 2016 11:58 UTC
Taimakon Italia ga jamhuriyar Nijar domin dalike hijirar da bata bisa doka.
Cibiyar Wata labaru ta "Africa Time" ta ambato cewa; Ministan harkokin wajen Kasar Italiya Paolo Gentiloni, da ya ke ziyarar aiki a jamhuriyar Nijar ya gana da shugaba Muhammad Isssoufou.
Ministan harkokin wajen na Italia ya gabatarwa da jamhuriyar Nijar kudi euro miliyan 200 a matsayin tallafi domin fuskantar matsalar yan gudun hijira.
Bugu da kari ministan harkokin wajen na kasar Italia ya jaddada wajabcin yin aiki tare da kasar Nijar domin karfafa cibiyoyin tsaro da kula da iyakoki da kuma ayyukan agaji.
Tarayya turai ta ware kudin da su ka kai Euro miliyan 500 domin fada da hijirar da ba ta bisa doka.
Tags