Sudan Ta Kudu Na Gab Da Fadawa Cikin Mummunan Yakin Basasa
Sakamakon rashin kasa samun daidaito da fahimtar juna tsakanin bangarorin da ba su ga maciji da juna a kasar Sudan ta kudu, hakan na neman ya sake jefa kasar a cikin wani mummunan rikici na yakin basasa.
Manzon musamman na majalisar dinkin duniya a kasar ne Adama Ding ya sanar da hakan a jiya a birnin Juba, inda ya ce a cikin 'yan kwanakin nan ya yi rangaji a sassa daban-daban na kasar, kuma ya zanta da jama'a daga dukkanin bangarori, gami da shugabannin kabilu a yankunan kasar, kuma abin da ya fahimta shi ne akwai babbar matsala da take tafe a kasar, matukar dai a ba a dauki matakan magance ta ba tun daga yanzu.
Ding ya ce matsalar ta samo asali ne daga irin tsananin gaba da ke tsakanin kabilu musamman ma manyan kabilun kasar guda biyu Dinka da kuma Nuweir, wanda kuma dukkanin matsalolin suna da alaka ne kai tsaye da batutuwa na siyasa, wadanda za a iya magance su idan aka kai zuciya nesa.
Babban jami'in na majalisar dinkin duniya ya ce akwai yankunan da a halin yanzu 'yan banga ne na kabilu suke iko da su, kuma suna cin karensu babu babbaka, kamar yadda wasu yankunan da suke karkashin ikon gwamnati tsirarun kabilu marassa rinjaye suke fuskantar tsangwama, akwai ma wasu yankuna da ake cin zarafin jama'a da kwashe dukiyoyinsu da kuma yi ma matansu fyade, wanda a cewarsa wadannan dukkaninsu alamu ne na halin rashin tabbas a kasar wadda har yanzu ba ta gama kafuwa a kan kafafunta ba, wanda kuma idan lamarin ya ci gaba da tafiya a haka, to zai kai ga sake maimaita irin abin da ya faru na kisan kiyashi a Rwanda a cikin shekara ta 1994, amma wannan karo a kasar Sudan ta kudu.
Wanann abin da yake faruwa a halin yanzu a kasar Sudan ta kudu na daga cikin abin da masana suka hango kan cewa zai iya faruwa tun kafin kasar ta balle daga kasar Sudan, amma duk da hakan kasahen yammacin turai da suke son cimma wata manufa ta su da hakan suka tsaya kai da fata wajen ganin Sudan ta kudu ta balle daga kasar Sudan, tare da kafa kasarta mai cin gishin kanta, wanda kuma bayan ballewar babu abin da wadannan kasashe suka tsinana ma Sudan ta kudu da al'ummarta.
Matsalar baya-bayan nan dai ta samo asali ne daga rikicin da ya kaule a birnin Juba, tsakanin jami'an sojin kasar da kuma magoya bayan madugun 'yan tawaye Reick Machar a cikin watan Yulin da ya gabata, bayan sulhun da aka yi tsakanin bangarorin biyu, wanda ya baiwa Machar damar sake komawa kan tsohon mukaminsa na mataimakin shugaban kasa, amma bayan wannan artabu, Machar ya bar Sudan ta kudu, kuma ga dukkanin alamu rikicin kasar zai sake komawa danye kamar yadda babban jami'in majalisar majalisar dinkin duniya ya yi hasashe.
Abin jira a gani a halin yanzu dai shi ne, irin rawar da kungiyar IGAD da kuma tarayyar Afirka gami da majalisar dinkin duniya za su iya takawa, domin kauce wa abin da ka iya faruwa a kasar, bayan wannan gargadi da babban jami'in majalisar dinkin duniya ya yi kan hakan.