Togo: Taron Wasu Kasashen Afirka Akan Harkokin Tsaro
Nov 13, 2016 08:34 UTC
Kasashe Biyar Na Yammacin Afirka Suna yin taro A Togo.
Kamfanin Dillacin Labarun Xinhua, ya ambato cewa; Jami'an tsaron, kasar Benin da Nijar da Burkina Faso, da Ivory Coast da Togo suna yin taro domin tattauna harkokin tsaro.
Jami'an tsaron kasashen biyar suna yin taron ne a birnin Lome inda su ke tattauna matsalar tsaro a cikin kasashen yammacin Afirka da kuma cikin kasashensu.
Jami'an tsaron kasashen suna kuma tattauna batun ta'addanci da fasakwaurin mutane da aikata manyan laifuka a cikn yankin na yammacin Afirka.
Wakilin kasar Togo a wurin taron Yark Damehane, ya bayyana cewa; Mahalarta taron sun daura azamar yin aiki tare a tsakaninsu domin fuskantar halin da ake ciki a yammacin Afirka.
Tags